Luke 11

Koyarwar Yesu a kan Adduʼa

1Wata rana Yesu yana adduʼa a wani wuri. Da ya gama, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Ubangiji, ka koya mana yin adduʼa, kamar yadda Yohanna ya koya wa almajiransa.”

2Sai ya ce musu, “Saʼad da kuke yin adduʼa, ku ce:

“ ‘Ya Uba,
sunanka mai tsarki ne
mulkinka ya zo.
3Ka ba mu kowace rana abincin yini.
4Ka gafarta mana zunubanmu,
kamar yadda mu ma ke gafarta wa duk wanda ya yi mana laifi.
Kada ka kai mu cikin jaraba.’ ”
5Saʼan nan ya ce musu, “Da a ce ɗayanku yana da aboki, saʼan nan ya je wurinsa da tsakar dare, ya ce, ‘Aboki, ranta mini burodi guda uku, 6domin wani abokina da yake tafiya ya sauka a wurina. Ga shi, ba ni da abinci da zan ba shi.’ 7Sai wanda yake cikin ɗaki ya amsa, ya ce, ‘Kada ka dame ni. An riga an kulle ƙofa, da ni da yarana kuwa mun kwanta, ba zan iya tashi in ba ka kome ba.’ 8Ina gaya muku, ko da yake ba zai so tashi ya ba shi burodin don shi abokinsa ne ba, duk da haka, zai tashi ya ba shi yawan abin da yake bukata, saboda nacewarsa.

9“Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 10Gama duk wanda ya roƙa, yana karɓa, mai nema yana samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma, za a buɗe masa ƙofa.

11“Wane mahaifi ne a cikinku, in ɗansa ya roƙe shi kifi, zai ba shi maciji a maimakon, 12ko kuma in ya roƙi ƙwai, ya ba shi kunama? 13In fa haka ne, ko da yake ku mugaye ne, kun san ba ʼyaʼyanku kyautai masu kyau, balle fa Ubanku na sama, zai yi fiye da haka, ta wurin ba da Ruhu Mai Tsarki, ga masu roƙonsa!”

Yesu da Beʼelzebub

14Saʼad da Yesu yake fitar da wani beben aljani daga wani mutum, da aljanin ya fita, sai mutumin wanda da bebe ne, ya yi magana, taron kuwa suka yi mamaki. 15Amma waɗansunsu suka ce, “Ai, da ikon Beʼelzebub, sarkin aljanu ne, yake fitar da aljanu.” 16Waɗansu kuma suka gwada shi, ta wurin neman ya nuna musu wata alama daga sama.

17Yesu kuwa ya san tunaninsu, sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa, zai lalace, kuma gidan da yake gaba da kansa zai rushe. 18In Shaiɗan yana gāba da kansa, yaya mulkinsa zai tsaya? Ina faɗin haka domin kun ce, da ikon Beʼelzebub nake fitar da aljanu. 19In da ikon Beʼelzebub nake fitar da su, to, da ikon wa masu binku suke fitar da su? Saboda haka, za su zama alƙalanku ke nan. 20Amma in da ikon Allah ne ni nake fitar da aljanu, ashe, mulkin Allah ya zo muku ke nan.

21“Saʼad da mutum mai ƙarfi, wanda yake da makamai yana gadin gidan kansa, an tsare lafiyar dukiyarsa ke nan. 22Amma in wani wanda ya fi shi ƙarfi, ya faɗa masa ya kuma sha ƙarfinsa, yakan ƙwace makaman da mutumin ke dogara da su, ya kuma rarraba ganima.

23“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni, wanda kuma ba ya tarawa da ni, watsarwa yake yi.

24“Lokacin da mugun ruhu ya fita daga mutum, sai ya bi ta wuraren da ba mutane, yana neman hutu, amma ya kāsa samu, sai ya ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ 25Saʼad da ya koma, ya tarar da gidan a share da tsabta, kuma a shirye. 26Sai ya je ya ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, sai su shiga su zauna a wurin. Ƙarshen wannan mutum kuwa zai fi farkonsa muni.”

27Da Yesu yake cikin faɗin waɗannan abubuwa, sai wata mace daga cikin taron ta ɗaga murya ta ce masa, “Mai albarka ce uwar da ta haife ka, wadda ka sha mamanta.”

28Yesu ya amsa, ya ce, “A maimakon, masu albarka ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma biyayya da ita.”

Alamar Yunana

29Da taron mutane suka ƙaru, sai Yesu ya ce, “Wannan mugun zamani ne. Tana neman wata abin banmamaki, amma ba ko ɗaya da za a ba ta, sai dai ta Yunana. 30Kamar yadda Yunana ya zama alama ga mutanen Ninebe, haka ma Ɗan Mutum zai zama ga zamanin nan. 31A ranar shariʼa, Sarauniyar Kudu za ta tashi tsaye tare da wannan zamani, ta yanke wa wannan zamani hukunci, domin ta zo daga ƙarshen duniya ta saurari hikimar Solomon, ga shi kuwa, shi wanda ya fi Solomon girma, na nan. 32A ranar shariʼa, mutanen Ninebe za su tashi tsaye tare da wannan zamani, su yanke wa wannan zamani hukunci. Gama sun tuba saʼad da Yunana ya yi musu waʼazi. Ga shi yanzu, shi wanda ya fi Yunana girma, na nan.

Fitilar Jiki

33“Babu wanda yakan ƙuna fitila saʼan nan ya ɓoye ta, ko ya rufe ta da murfi ba. A maimako, yakan ajiye ta a kan alkuki, don masu shiga su ga haske. 34Idonka shi ne fitilar jikinka. Saʼad da idanunka suna da lafiya, dukan jikinka ma na cike da haske, amma saʼad da idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma na cike da duhu. 35Ka lura fa, kada hasken da yake cikinka ya zamana duhu ne. 36Saboda haka, in dukan jikinka yana cike da haske, ba inda ke da duhu, jikinka kuwa zai kasance da haske gaba ɗaya, kamar yadda hasken fitila yake haskaka ka.”

Laʼanu Guda Shida

37Da Yesu ya gama magana, sai wani Bafarisiye ya gayyace shi cin abinci tare da shi. Sai kuwa ya shiga ya zauna a tebur. 38Amma Bafarisiyen ya lura cewa, Yesu bai wanke hannu kafin ya ci abinci ba, sai mamaki ya kama shi.

39Sai Ubangiji ya ce masa, “Ku Farisiyawa, kukan wanke bayan kwano da kwaf, amma a ciki kuna cike da kwaɗayi da mugunta. 40Ku wawayen mutane! Ashe, wanda ya yi bayan, ba shi ne kuma ya yi cikin ba? 41Ku ba matalauta abin da yake cikin kwano, kuma kome zai zama muku da tsabta.

42“Kaitonku, Farisiyawa, domin kuna ba wa Allah zakka na anananku, da ƙarƙashinku, da kuma sauran ganyen lambunku iri-iri, amma kun ƙyale adalci da ƙaunar Allah. Ya kamata da kun kiyaye na ƙarshen, ban ba barin na farkon.

43“Kaitonku, Farisiyawa, domin kun cika son wuraren zama masu daraja a majamiʼu, da kuma yawan gaisuwa a wuraren kasuwanci.

44“Kaitonku, domin ku kamar kaburbura ne da ba a sa musu alama ba, waɗanda mutane suke takawa don rashin sani.”

45Sai ɗaya daga cikin masanan dokoki ya ce wa Yesu, “Malam, in ka faɗi waɗannan abubuwa haka, kai kuma ka zage mu ke nan.”

46Yesu ya amsa, ya ce, “Ku masanan dokoki ma, kaitonku, domin kun ɗora wa mutane kaya masu nauyi waɗanda da ƙyar suke ɗaukawa, amma ku da kanku ba za ku sa ko yatsa ɗaya, don ku taimake su ba.

47“Kaitonku, domin kun gina kaburbura saboda annabawa, nan kuwa kakannin-kakanninku ne suka kashe su. 48Wannan ya shaida cewa kun amince da abin da kakannin-kakanninku suka yi. Sun karkashe annabawa, ku kuma kun gina kaburburansu. 49Saboda haka, Allah a cikin hikimarsa, ya ce, ‘Zan aika musu da annabawa da manzanni. Za su kashe waɗansu, su kuma tsananta wa waɗansu.’ 50Saboda haka, alhakin jinin dukan annabawa da aka kashe, tun farkon duniya, yana kan wannan zamani, 51wato, tun daga jinin Habila, har zuwa jinin Zakariya, wanda aka kashe tsakanin bagade da mazauni. I, ina gaya muku, alhakinsu duka yana kan wannan zamani.

52“Kaitonku, masanan dokoki, domin kun ɗauke mabuɗin ilimi. Ku kanku ba ku shiga ba, kuma kun hana wa waɗanda suke shiga, su shiga.”

53Da Yesu ya bar wurin, sai Farisiyawa da malaman dokoki suka fara gaba mai tsanani da shi, kuma suna tsokanansa da tambayoyi. 54Suna fakonsa, don su kama shi a kan wata magana da zai faɗa.

Copyright information for HauSRK